bootwax.pages.dev


Sadiya gyale biography of abraham

Sadiya gyale biography of abraham: You 're really looked gleamingly

L atsa alamar lasifika da ke sama domin sauraren hira da Sadiya Gyale. Fitacciyar jarumar fina-finan Kannywood Sadiya Gyale, ta ce masu yin amfani da sunanta suna yada labaran karya suna matukar bata mata rai. A watan Yuli ne aka rika yada jita-jita a kafafen sada zumunta cewa jarumar ta mutu a asibitin Malam Aminu Kano da ke arewacin Najeriya.

Gaskiya yadda ake amfani da sunana ana bata min suna yana damu na matuka. Abin da ta fada wa BBC lokacin da aka ba da rahoton rasuwar ta. Sadiya ta shaida wa BBC cewa, ita dai tana zaman-zamanta da lafiyarta, sai kawai taga ana ta kiranta a waya ana tambayarta ko lafiya don ga labarin da ke yawo a kafafan sada zumunta. Ta ce tun tana daukar abin kamar wasa, sai kuma ta ga cewa lallai an yada labarin cewa ta mutun.

Ta ce labarin mutuwarta ta da aka yada ya sa masoyanta da dama cikin tashin hankali, domin kuwa wasu daga cikinsu ko baccci kasa yi suka yi, wasu kuma a ranar ko abinci ba su iya ci ba inji ta. Sadiya ta ce, ita agaskiya labarin sam bai dame ta ba, don kuwa a ranar ma bacci ta yi har da mun shari, domin ta san cewa dukkan mai rai mamacine wata rana.

Jarumar ta ce wadanda suka mutu ba gaggawa suka yi ba, haka wadanda suke raye ma ba jinkiri suka yi ba, fatan ta Allah ya sa ta cika da kyau da imani. Sadiya Gyale, ta ce a gaskiya irin yada wadannan labarai na karya sam ba dai-dai ba ne a cikin al'umma musamman musulmai. Ta ce "A gaskiya duk wanda ko wadda ta shirya wannan labari, to ta daukarwa kanta ko kansa babban alhaki, kuma ba bu wata riba da mutum zai samu a kan hakan".